Ainihin Labarin Yesu
Kalli Gaskiyar Labarin Yesu
Ziyara Zuwa Shafin
Mutane sunyi Addu'a
Kalli Labarai iBIBLE
Idan ka yi addu'ar ceto yanzu kai ɗan Uba mai duka ne.
"Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Ubamaiduka ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto." —Romawa 10:9
Kana iya yin addu'a tare da mu a yanzu don cetonka:
Ya Uba mai duka,
Na furta cewa Yesu Ubangiji ne. Na gaskanta an haife shi daga budurwa, ya mutu akan giciye domin zunubai na, kuma ya tashi daga matattu bayan kwana uku. Yau, na furta cewa na yi maka zunubi, kuma ba abin da zan iya yi domin in ceci kaina. Ina roƙonka ka gafarta mini, kuma na dogara ga Yesu kaɗai. Na yi imani cewa yanzu ni ɗan Ka ne kuma zan dawwama tare da Kai har abada. Ka bi da ni kowace rana da Ruhu Mai TsarkinKa. Ka taimake ni in ƙaunace Ka da dukan zuciyata, raina, da hankalina in kuma ƙaunace wasu kamar kaina. Na gode da ka cece ni ta wurin jinin Ɗan Ka, Yesu. A cikin sunan Yesu na yi addu'a. Amin.